Connect with us

Barka Da Hantsi

Muna nan a kan bakanmu na tsunduma yajin aiki – JUHESU

Published

on

Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikantan lafiya ta kasa reshen jihar Kano JUHESU ta ce, ba gudu ba ja da baya kan kudirin ta na tsunduma yajin aiki.

Ƙudurin Ƙungiyar ya biyo bayan gaza cika mata alƙawuran da gwamnatin tarayya ta ƙi yi mata.

Shugaban kungiyar JUHESU reshen asibitin Aminu Kano Murtala Isah Umar ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan Freedom Radiyo, da ya mayar da hankali kan abubuwa da ke janyo yawan tafiya yajin aikin likitoci.

Murtala Isah ya ce, “gwamnatin tarayya ta sha daukar mana alkawari na cika mana buƙatun mu amma kuma har yanzu batai ɗaya daga ciki ba”in ji Pharmacist Murtala Isa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!