Connect with us

Labarai

Mutane 72 sun rasa rayukansu bayan bullar cutar zazzabin Lassa

Published

on

Cibiyar kula da cututtuka ta kasa ta ce mutane saba’in da biyu ne suka rasa rayukansu tun bayan bullar cutar Lassa Fever a ranar daya ga watan Janairun wannan shekara.

Hakan na kunshe ne ciki wani rahoto kan halin da ake ciki game da bullar cutar Lassa Fever a kasar nan wanda cibiyar ta fitar Larabar da ta gabata a Abuja.

Rahoton ya bayyana cewa an samu bullar cutar ta Lassa Fever ne a jihohi goma sha takwas na kasar nan kuma mutane dubu daya da tamanin da daya ne suka kamu da cutar.

Jihohin da aka samu bullar cutar a cewar cibiyar sun hada da: Edo da Ondo da Bauchi da Nassarawa da Anambra da Ebonyi da Benue da kuma Kogi.

Sauran sune: Imo da Plateau da Lagos da Taraba da Delta da Osun da Rivers da birnin tarayya Abuja da Gombe da kuma Ekiti.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,677 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!