Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nan ba da jimawa ba za’a cigaba da buga Mujallar News Track-NUJ

Published

on

Shugaban kungiyar yan jaridu na jihar Kano kwamared Abbas Ibrahim ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai farfado da Mujallar ‘yan jaridu mai suna ‘’News Track’’.

Shugaban kungiyar ‘yan jaridun ya bayyana hakan ne litinin din nan yayin da ya karbi bakuncin tawagar shugabannin kungiyar ta NUJ reshen tashar Freedom Radio a sakatariyar kungiyar.

Kwamared Abbas Ibrahim ya ce kokarinsa na samar da kudin shiga ga kungiyar ne ya sanya shi tunanin farfado da Mujallar wadda aka jima ba a waiwaye ta ba.

Shugaban na kungiyar NUJ ta Kano ya kuma yaba wa tashar Freedom inda ya ce ita ce tashar da ta kafa reshen kungiyar ba tare da an kai ruwa rana ba tsakanin shugabannin tashar da kuma ma’aikatanta.

A jawabin sa tun farko, shugaban kungiyar ta Yan jaridu reshen tashar Freedom Radio Abubakar Abdulkadir Dangambo ya yi kira ga sabon shugaban na NUJ ya samar da matakan kakkabe baragurbin yan jarida dake bata sunan aiki a jihar Kano.

Abubakar Dangambo ya kuma ce makasudin ziyarar shi ne don jaddada goyon bayan mambobin kungiyar ta NUJ na Freedom ga sabon shugaban wanda ya kama aiki makon da ya gabata, inda har ma ya bukaci shugaban kan ya samarwa kungiyar hanyar samun kudin shiga ta hanyar amfani da filin sakatariyar don gina wuraren sana’a kamar yadda ya gani a wasu daga cikin sakatariyar ‘yan jaridun wasu jihohin Najeriya.

Shugaban kungiyar na tashar Freedom ya bukaci shugaban kan ya dage wajen shirya babban taron kungiyar domin bada dama ga dukkan mambobi su rika shiga ana damawa da su a cikin al’amuran kungiyar ba tare da an tauye musu wani hakki ba.

Da yake bada amsa kan lamarin, Kwamared Abbas Ibrahim ya ce kungiyar tana da cibiyar kasuwancin na’ura mai kwakwalwa mai dauke da sabbin kwamfutoci sai dai a baya ba’a fara amfani da su ba amma a yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa wajen fara amfani da wurin tare da fara bada horo kan ilimin kwamfuta tare da yin amfani da wurin wajen mayar da shi cibiyar bincike tare da adana bayanai kan abubuwan da suka shafi aikin jarida.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!