Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kimiyya

NEMA : Za’a fuskanci ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa

Published

on

Hukumar bada Agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bukaci mazauna jihohin Zamfara da Sokoto da Kebbi  da su kaucewa zubar da shara  barkatai domin gujewa afkuwar ambaliyar ruwa da take barazana ga jihohinsu.

Babban darakta a hukumar Muhammad Alhaji Muhammad ne ya bayyana hakan yayin taron gangamin wayar da kai da hukumar ta shirya da hadin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara.

A cewarsa sakamakon  yawan ruwan sama da ake samu yasa hukumar ta ga dacewar shirya gangamin domin wayar da kan al’umma akan mahimmacin tsaftar muhalli da kuma amfanin yashe magudanan Ruwa.

Da yake jawabi kwamishinan muhalli a jihar ta Zamfara, Dakta Nuraddeen Isah, ya ce, wayar da kan al’ummar jihar zai taimaka sosai wajen magance matsalar ambaliyar ruwa dake barazana ga jihar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!