Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Niger:yan bindinga sun sace wasu yan kasuwa 18 a garin Pandogari

Published

on

‘Yan bindiga sun sace wasu ‘yan kasuwa guda goma sha takwas wadanda su ka bar garin Pandogari a kan hanyar su ta zuwa Bassa da ke yankin karamara hukumar Rafi a jihar Niger.

 

Rahotanni sun ce mutanen suna kan hanyar su ce ta zuwa garin na Bassa domin cin kasuwa.

 

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da ya kubuta daga hannun ‘yan bindigar, ya shaidawa manema labarai cewa, suna cikin tafiya ne cikin wata motar safa, sai kawai su ka ci karo da wani shingen binciken ababen hawa da ‘yan bindigar su ka shirga, akan titi, sannan su ka yi ta harba bindiga sama wanda a dalilin haka suka tursasa direbar motar ya tsaya.

 

A cewar sa, bayan da motar ta tsaye ne, ‘yan bindigar suka tursasa mutanen da ke cikin ta, suka fita su ka koma cikin wata motar ta daban wanda kuma daganan ta shiga cikin daji.

 

Iyalan ‘yan kasuwar sun shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun bukaci da a biya su kudin fansa, da ya kama daga naira dubu dari biyu zuwa dubu dari biyar akan kowanne mutum guda.

 

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Niger, Muhammed Abubakar, ya ce, sun samu labarin faruwar lamarin, amma a hukumance jami’ansu da ke yankin ba su sanar da su halin da ake ciki ba, sai dai duk da hala sun tura da jami’ai na musamman zuwa yankin, domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!