Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Nuna banbanci:SSANU DA NASU sun gudanar da zanga zanga

Published

on

Gamanyyar kungiyoyin SSANU da NASU reshen jami’ar Bayero da ke nan Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana kan yadda ake fifita kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa ASUU wajen rabon kuɗaɗen alawus na wata wata.

Kungiyoyin sun gudanar da zanga-zangar ne a harabar jami’ar Bayero da ke nan Kano da tsakar ranar Alhamis.

Da yake jawabi yayin zanga-zangar shugaban kungiyar ta SSANU reshen jami’ar Bayero kwamared Mustapha Aminu ya ce, ko kaɗan ba a yi musu adalci ba, kan yadda ake fifita kungiyar ASUU a kansu duk da cewa mambobinsu sunfi yawa.

Shima shugaban ƙungiyar SSANU Kwamared Abdullahi Nasir ya ce ko dai a duba kokensu ko kuma su dauki matakin da ba zai yiwa kowa dadi ba.

Ya yin zanga-zangar, ƴan ƙungiyar sun yi tattaki daga sakatariyar su zuwa harabar ofishin shugaban jami’ar domin mika masa takardar kokensu a rubuce

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!