Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Rundunar sojojin sama ta dakile wasu ayyukan mayakan Boko-Haram

Published

on

Rundunar sojojin saman kasar nan, ta ce; ta dakile ayyukan mayakan Boko-Haram a yankunan Bulagalaye da Kwakwa a jihar Borno sakamakon hare-hare da ta yi ta kaiwa ta sama.

Daraktan yada labarai na rundunar Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ta cikin wata sanarwa, ya ce; an kai hare-haren ne a ranar Lahadin makon jiya.

Ya ce sun samu nasara sosai wajen hare-haren, ba ya ga wadanda suka kashe wasu sun tsere da raunuka a jikin su.

Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ta cikin sanarwar ya kara da cewa, tun da fari sun samu rahotannin asiri da ke cewa mayakan na Boko-haram sun yi tunga a wani waje da ke yankin, lamarin da yasa suka tura da jirage domin kai musu hari.

Sanarwar ta kuma bukaci al’ummar kasar nan musamman mazauna yankunan da ke fama da matsalar tsaro da su rika sanar da rundunar da zaran sun ga bakin fuska a yankunan su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!