Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta dawo da jami’ai da suka rage na Majalisar dinkin Duniya a Liberia

Published

on

Rundunar ‘yan-sandan Najeriya ta janye tawagarta ta karshe mai dauke da jami’ai 108 da ta rage cikin shirin samar da zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya a kasar Liberia bayan shafe tsawon shekaru biyar suna aiki a can.

A cikin watan Fabarairun jiya ne dai Najeriya ta janye jami’anta 200 daga cikin shirin a wani bangarena kawo karshen aikin da Majalisar dinkin Duniya a can, kamar yadda rundunar ta tabbatar.

Tun a cikin shekarar 2003 ne dakarun tsaron kasar nan suka kasance a Liberia lokacin aka samar da Rundunar tsaron domin wanzar da zaman lafiya inda Najeriya ta kasance babbar mai bada gudunmasa a shirin.

Manufar shirin ita ce kawo karshen karan tsaye da ake yi wa doka da oda da kyautata kare hakkin bil’adama duka dai domin samar da zaman lafiya mai dorewa, wanda kuma shirin zai kawo karshe a ranar 30 ga watan Maris din nan da mu ke ciki na shekarar 2018.

Babban jami’in tsaro daga Najeriya Manjo Janar Salihu Uba ne kwamnadan rundunar da ta kunshi jami’ai maza da mata daga kasashen Pakistan da Ukraine da kasar nan har ma da wasu kasashe na daban.

Shugaban Liberia George Weah ya godewa rundunar bisa jajircewarta wajen tabbata da zaman lafiya a kasar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!