Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar yan sanda ta kame wasu gaggan yan fashin da suka addabi bankuna

Published

on

Rundunar yan sanda ta kame wasu gaggan yan fashin da suka akaita fashi a bankunan garin Offa na jahar Kwara da ya faru a watan Afrilun bana.

Wadanda rundunar ta kame sun hada da Micheal Adikwu dan asalin karamar hukumar Apa da ke jahar Benue da kuma wani korarren dansanda da aka kora tun shekarar 2012 saboda sanadin da yayi na sakin yan fashi a shekarar 2012.

Shi dai wannan dan fashin ya samu fita daga dauri ne a shekarar 2015 inda ya zama rikakken dan fashi sannan kuma an kame shi  a sati biyu da suka wuce.

Duk wadanda aka kame din sun amsa zargin da ake yi musu na yin fashi a Bankin da ke garin Offa ta jahar Kwara.

rahotonni sun bayyana cewa Kame yan fashin ya yi nasara ne sakamkon buga hotunansu a kafafen yada labaran kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!