Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta musanta cewa tana da hannu a rikicin majalisar dokokin jihar

Published

on

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Akwa Ibom Musa Kimo ya musanta cewa rundunar ‘yan sandan jihar na da hannu wajen rikicin da majalisar dokokin jihar ta fada tun daga ranar 19 ga wannan wata.

Musa Kimo ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga manema labarai kan rikicin da ya afko na ranar 27 bayan da aka garkame majalisar.

A cewar sa jami’an ‘yan sanda za su gudanar da ayyukan su ba tare da nuna son zuciya ba ga kowanne bangare.

Haka zalika kwamishinan ‘yan sanda ya gargadi ‘yan siyasa da magoya bayan jam’iyyu a jihar ta Akwa Ibom da su guji tada hautsani da rikici da sauran ayyukan ta’addanci, don kawo zaman lafiya a jihar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!