Connect with us

Labarai

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutane 7

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai yayin wani Sabon hari da wasu yan bindiga suka kai a kauyen Gidan-labbo da gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

 

Jami’in yada labaran rundunar yan sandan DSP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a jiya Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

 

Ya ce wadan su yan bindiga ne da ba a kai ga tantance ko su waye ba suka hari wasu mutane a dajin Malikawa a lokacin da suke kokarin gyara gonakin su domin tunkarar damunar bana.

 

D S P Shehu ya ce rundunar yan sandan da sauran jami’an tsaro sun aike da rundunar su zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya.

 

Ya kuma bukaci al’ummar yankin da su cigaba da bai wa jami’an tsaro hadin kan da ya da ce, tare da mika rahoton duk wani motsi da basu yar da da shi ba domin hakan zai taimaka musu wajen kawar da bata garin.

 

Haka kuma anjiyo gwamnan jihar ta Zamfara Abdul’aziz yari na cewar yan bindigar sun aike da takardar gargadi ga manoma a fadin jihar, inda suka nemi da su kauracewa gonakin su a kowanne hali.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,589 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!