Labarai
Rusau: Kotu ta umarci Abba Gida-gida ya biya diyyar biliyan 30.
Babbar kotun yarayya da ke zamanta a gyaɗi-gyaɗi ta umarci gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya biya diyyar Naira biliyan talatin sakamakon rusau da ya yi.
Kotun ƙarkashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda ne ya zartar da hukunci a kan ƙarar da ƙungiyar masu shaguna a jikin masallacin Idi suka shigar gabanta, inda suke ƙalubalantar matakin rushe musu shaguna da gwamnatin ta yi.
Da yake zartar da hukuncin mai shari’a Amobeda ya ce matakin rushe shagunan ya saɓa da doka kuma ba’a yi shi bisa la’ida ba.
A don haka kotun ta umarci gwamnatin Kano da ta biya masu shagunan naira biliyan 30, tare da hana gwamnatin shiga ko kuma bayar da filin ga kowanne mutum ta kowacce siga.
Barista Dakta Nuhu Ado Ayagi shi ne Lauyan masu ƙara, ya ce “hukuncin ya yi musu daidai da abinda suke fata, domin an jefa masu kasuwanci a wajen cikin ƙangin rayuwa.”
A nasa ɓangaren kwamishinan Shari’ah na jihar Kano Barista Haruna Isah Dederi ya ce “Tuni suka shirya matakin ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun domin kuwa bai yi daidai da matakin da ya sa gwamnatin ta yi rusau ba”.
A baya dai gwamnatin Kano bayan ta rushe shagunan da aka yi a filin Idin, ta shirya ƙulla yarjejeniya da wani kamfani a Saudiyya don yin tasarrafi da filin Idi ta wata siga.
You must be logged in to post a comment Login