Labarai
Sabuwar manhajar yaɗa labarai za ta inganta al’adun ƴan Najeriya – Lai Muhammad
Gwamnatin tarayya ta ce samar da sabuwar manhajar tashoshin kallon talabijin kyauta ta zamani zai bunƙasa al’adun al’ummar Najeriya.
Ministan yaɗa abarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da manhajar a gidan gwamnatin Kano ranar Talata.
“Muna sane da yadda tashoshin talabijin na ƙasashen ƙetare ke sauya al’ummar kasar mu bakin al’adu, hakan ya sa muka ga dacewar samar da manhajar”.
“Manhajar za ta bai wa al’ummar kasar nan musamman ma matasa masu basira damar nuna kan su don su amfana da ita”.
“Kuma Tattalin arziƙin ƙasa zai ƙari a Najeriya dalilin amfani da fasahar zamani”.
Kazalika Lai Muhammad ya ce za’a rinka kallon tashoshin da ke kan Manhajar kyauta ga wanda ya ke amfani da ita.
“Manhajar dama ce ga masana’antar shirya fina-finai da mawaƙa da malamai damar isar da saƙon su cikin sauki ga al’umma”.
Ministan ya kuma ce, tashar za ta bai wa al’ummar ƙasar nan da ke gudanar da sana’oin dogaro da kai musamman wanda al’ummar kasar ke gudanarwa tuntuni damar inganta sana’ar su.
You must be logged in to post a comment Login