Connect with us

Labaran Kano

Sarkin Benin ya bukaci gwamna Ganduje ya yi nazari kan sabbin masarautu

Published

on

Sarkin Benin , Oba Ewuare II ya bukaci gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya sake nazari dangane da Karin sabbin masarautun jihar Kano.

Sarkin ya bayyana haka ne a jiya lokacin da suka kai ziyara fadar gwamnatin jihar Kano.

Ya ce abin damuwa ne karin sabbin masarautun jihar Kano, inda ya bukaci gwamnan da ya sauya ra’ayin sa na wannan kari,  ya kara da cewa a zantawarsu da gwamnan ya nuna yiwuwar duba kan wannan batu.

Inda ya ce za su duba yiwuwar hakan, sarkin na Benin ya ce, yana magana da yawun bakin ‘yan uwansa  na rokon gwamnan da ya sake tunani kan wannan al’amari na Karin masarautu a jihar Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!