Connect with us

Kiwon Lafiya

Sashen kula da albarkatun man fetur ya musanta zargin cewar an bada lasisi guda 38

Published

on

Sashen kula da Albarkatun man fetur na kasa DPR, ya musanta rahotannin da kafafen yada labaran kasar nan suka yada cewa, ya ba da lasisi guda 38 ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu domin kafa kananan matatun mai.

A cewar DPR lasisi 25 kacal ya ba da ba 38 ba kamar yadda aka yi ta yadawa tun da fari.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sashen ya aikewa manema labarai jiya a Abuja.

A cewar sanarwar daga shekarar 2002 zuwa yanzu masu sha’awar gina kananan matatun mai 105 ne suka mika da bukatar su.

Sashen kula da Albarkatun man fetur din ta cikin sanarwar dai, ya kuma ce, an baiwa ‘yan kasuwar wa’adin watanni goma sha takwas ne domin kammala aikinsu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,906 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!