Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shari’ar Abduljabbar: Lauyoyin Gwamnati sun ci gaba da gabatar da shaidu a gaban kotu

Published

on

A ranar Alhamis 28 ga watan Oktoba, lauyoyin gwamnati 12 suka sake gabatar da shaida na biyu a gaban kotu kan ƙarar da gwamnatin Kano ta shigar da Abduljabbar.

Lauyoyin ƙaƙashin jagorancin Barista Siraja Sa’ida SAN suka bayyana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke zaman ta a Ƙofar Kudu ƙarƙashin mai shari’a Ibrahim sarki yola

Bayan kammala sauraron shaidar ne lauyoyin Abduljabbar Nasir Kabara bisa jagorancin Muhammad Aminu Mika’ilu suka roƙi kotun ta sahale musu Abduljabbar ɗin ya yiwa shaidar tambayoyi da kansa.

Sai dai lauyoyin da ke ƙara ba su yi suka kan wannan buƙata ba.

Waɗanda aka karɓi shaidar sai Murtala Kabir Muhammad, ɗan unguwar Ƙofar Na’isa lokon maƙera mai shekaru 31, yana sana’ar koyarwa.

Kafin fara sauraran shaidun sai da masu ƙara suka mayar da martani kan batun hurumin da lauyoyi masu lambar SAN na tsayawa a kotun.

Inda lauyayin abduljabbar ɗin suka ce za su mai da martani a zama na gaba.

Tun a makonni biyu da suka gabata ne masu ƙara suka gabatar da shaida ɗaya, inda anan ne kuma kotun ta tafi hutu don yin nazari a kan batun.

Bayan dawowa daga hutu mai Sharia Sarki Yola ya yi ƙwaryaƙwayar hukunci inda ya ce, “sai dai Abduljabbar ya zaɓi ɗaya ko ya tsayawa kansa har ƙarshen shari’ar sannan kuma ya sallami lauyoyin sa, ko kuma ya yi shiru lauyoyin sa su tsaya masa.

A nan ne ya ce, “Ni shari’ata ba ta lauyoyi ba ce ta hadisai ce, ba wani lauya da zai iya tsaya mun, hasali ma cikin lauyoyin na wanda ya san larabci ko larabcin bai iya karantawa ba bare ya fahimce shi, don haka na cire su.

Sai dai lauyan masu ƙara Barista Sirajo Sa’ida SAN ya yi suka kan batun inda ya ce tuhumar da ake masa in ta tabbata hukuncin kisa ne, dan haka ba zai yiwuwa ayi shari’a babu lauyoyin da za su tsaya masa ba.

Dan haka ya roƙi da a saka wata ranar domin kowanne ɓangare su duba abin a nutse.

Bayan fitowa daga kotun lauyan mai ƙara Barista Mammam Lawan Yusufari ya ce “Daga ɓangaren mu mun amincewa Abduljabbar yayiwa shaidu tambayoyi da kan sa, sai dai alƙali yaƙi amincewa har ma ya ce in yana so ya yi da kan sa sai dai ya sallami lauyoyin sa”.

“A ƙa’idar shari’a ba sa yin ta sai da lauya, don haka muka nemi a ɗaga ƙarar, don haka za mu yi shawara don ganin yadda za a ci gaba da ƙarar ba tare da lauyoyin sa sun fita ba”.

Ana kuma sa ranar 11-11-2021 don ci gaba sannan kotun ta yi umarni da a sake gabatar da shaida na biyu a gaban kotun domin amsa tambayoyi ga ɓangaren wanda ake ƙara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!