Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shari’ar ta baiwa iyaye damar yiwa ‘yayansu auren fari

Published

on

Wani lauya mai zaman kansa a nan kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce shari’ar musulunci ta halastawa iyaye yiwa yayansu auren fari,  Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin shari’a a aikace day a gudana a  gidan Rediyon Dala da safiyar yau.

Umar Usman Dan Baito, yace kamar yadda iyaye suke da hakki akan ‘ya yansu, haka suma ya’yan suke da hakki akan iyayen nasu, wanda kuma daya daga ciki shine iyayen su yiwa ya’yan auren fari, amma idan dan yana son zai kara auren sai yayi da kansa kasancewar na biyun baya daga cikin hakkinsu.

A zantawar da wakilin mu Buhari Isah, yayi da wasu samari a nan kano mafi yawa sun nuna sha’awarsu da ayi musu auren, a yayin da kaso mafi karanci kuma suka nuna basu da bukatar hakan matukar dai basu da sana’ar rike iyalin.

A bangaren wasu iyaye maza kuwa da wakilin namu ya zanta dasu sun bayyana aniyarsu ta yiwa ‘ya’yan nasu auren inda suka bayyana farin cikinsu matukar dai suna da sukunin yi musu yin hakan.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!