Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Shekaru Biyu: An yi jimamin rashin Tijjani Ado Ahmad

Published

on

A ranar 30 ga watan Satumban shekarar 2017 Allah ya karbi rayuwar Tijjani Ado Ahmad a wani asibiti dake birnin Altlanta na kasar Amurka sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

Tijani Ado Ahmad ya kasance ma’aikacin gidan Rediyo Freedom dake Kano wanda yake gabatar da shirye- shirye da dama, ciki kuwa harda shahararren shirin nan da ake kira da  suna Barka da Hantsi da kuma shirin turanci mai taken Greetings from America.

Marigayi Tijjani Ado Ahmad ya bada gudunmawa sosai wajen kawo ci gaban al’umma a aikin jarida ta hanyar wayar da kan  mutane kan al’amuran yau da kullum.

A ranar 23 ga watan satumban shekarar ta 2017 ne Marigayi Tijjani Ado ya tafi kasar Amurka don amsa gayyatar da ofishin jakadancin kasar Amurka suka yi masa, kwanaki kadan bayan ya dawo daga kasar Saudiya inda ya gudanar da ibadar aikin Hajji.

A kuma ranar 30 ga watan na Satumba Allah ya karbi rayuwar sa a wani asibiti dake birnin Altanta dake kasar ta Amurka.

Ya rasu yana da shekaru 39, ya bar mace guda  da ‘ya’ya 2.

Sai dai ba a samu damar gudanar da jana’izar marigayin ba sai bayan kwana 21 da rasuwarsa, wanda hakan na da alaka da tsarin kasar Amurka wajen fita da gawar mamaci bayan ya rasu a can, kasancewar sai da ‘yar ’uwar marigayin taka je har kasar ta Amurka sannan aka dawo da gawar sa nan gida Najeriya.

Da yammacin ranar talata 24 ga watan Oktoba gawar marigayi Tijjani Ado Ahmad ta iso Kano inda aka gudanar da sallar jana’izarsa a Kofar Kudu dake fadar mai martaba Sarkin Kano.

Dubban al’umma ne suka halaraci sallar jana’izar wadda Babban limamin Kano Farfesa Muhammad Sani Zahraddin ya jagoranta, ciki kuwa har da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na II da Mataimakin gwamnan jihar Kano a wancan Lokaci Farfesa Hafizu Abubakar.

Wasu daga cikin abokan aikin Marigayi Tijjani Ado Ahmad sun bayyana kadan kadan daga cikin Halayen Marigayin.

 

Salisu Baffayo:

“Tun Ranar 21 ga watan Augusta har zuwa ranar 19 ga Satumbar shekarar 2017 Babu abin da ke raba ni da Tijjani Ado Ahmad a kasa mai tsarki , bayan mun kasance a mazuni guda a jirgi, tare muke zuwa Harami kafata- kafarsa har muka gama gudanar da Ibada. Hakika nayi rashin dan uwa, abokin aiki, abokin shawara kuma abokin gwagwarmaya.

Nasir Salisu Zango :

‘   Marigayi Tijjani Ado Ahmad ya kasance mutuum mai Hakuri, ba shi da abokin fada sannnan yana da jajircewa wajen neman na kasance. Ya kasance mai biyayya ga manya kulllum cikin maganar mahaifiyarsa. Hakika Tijjani Ado Ahmad ya bar gibi da ba za a iya cikewa ba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!