Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya amince da nadin wasu manyan alkalai 28

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin wasu manyan alkalai 28 a babbar kotun daukaka kara da kuma babbar kotun tarayya da kuma babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa sahalewar majalisar alkalai ta kasa.

Cikin alkalai goma sha biyu da aka amince dasu su shugaban ci babbar kotun daukaka kara ta kasa akwai mai shari’a Patricia A Mahmud da ta fito daga nan Kano sai kuma mai shari’a A S  Umar da sauran wasu alkalai goma.

Haka kuma an nada wasu alkalan a babbar kotun tarayya su tara da suka hadar da Sa’adatu Ibrahim Mark, da kuma Aminu Baffa Aliyu, sai kuma Tijjani Garba, da sauran wasu mutane biyar.

Kazalika Binta Muhammad na daga cikin alkalan babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja tare da Babangida hassan da kuma Samira Umar Bature da wasu mutum hudu.

Haka kuma ana sa ran babban jojin kasar nan Walter Onnoghen ne zai rantsar da sabbin alkalan kotun daukaka karar gobe Juma’a da misalin karfe 10 na safe.

Ka zalika alkalan babbar kotun tarayya za a rantsar da su a ranar 25 ga watan da muke ciki da misalin karfe 2 na rana yayin da sabbin alkalan kotun daukaka kara da ke birnin tarayya Abuja kuma za a rantsar da su a ranar 26 ga wannan wata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!