Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Siyasa

Shugaba Buhari ya bukaci daukar tsauraran matakai kan masu yada kalaman batanci

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a dauki tsauraran matakai kan kafafen sada zumunta na zamani da mutane ke amfani da su wajen yada kalaman batanci da rura wutar rikici a fadin duniya.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne jiya Laraba yayin da yake gabatar da jawabi a taron zauren majalisar dinkin duniya karo na 74 wanda ke gudana a birnin New York na kasar Amurka.

Ya ce, da dama daga cikin tashe-tashen hankula da ake fama da su a sassa duniya wadannan kafafe ne ke haddasa su, bisa yadda wasu ke yada kalaman da ke haddasa fadace fadace da tayar da hankalin al’umma.

Muhammadu Buhari ya kuma bukaci takwarorinsa na sauran kasashe da su hana yada kalaman kiyayya da na sukar addinai da ake yadawa a shafukan na sada zumunta na zamani wanda ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi baya ga raba kan kasashe.

Haka kuma ya bayyana cewa, ko a yanzu haka gwamnatinsa na fuskantar matsaloli wajen yaki da cin hanci da rashawa musamman kan hukuncin da wata kotun Amurka ta yanke na biyan kamfanin P&ID diyyar fiye da Dala biliyan 9 sakamakon wata yarjejeniya da ya kira da haramtacciya da shugabannin Najeriya suka kulla da kamfanin a shekarar 2010.

Ya kuma bukaci da a zage damtse wajen ganin an magance matsalolin masu tsattsauran ra’ayi da safarar mutane da kuma cin hanci da rashawa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala kalaman nasa da cewa talauci shi ne babban abinda ke addabar kasashe masu tasowa, wanda ya zama dole a tashi tsaye wajen ganin an magance shi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!