Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya bukaci Sojoji su hada da sauran jami’an tsaro don magance kunar bakin wake

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Sojoji su hada kai tare da sauran jami’an tsaro wajen bullo da sabbin dabaru domin kawo karshen aikin masu hare-haren kunar bakin wake a kasar nan.

Shugaban kasa na fadin hakan ne a jiya Litinin yayin da yake bude taron bikin shekara-shekara na manyan jami’an Sojoji a birnin Badin na Jihar Oyo, wanda za su shafe tsawon mako guda suna wasa kwakwalwa kan al’amuran da suka shafe su.

Taron dai yana baiwa Sojojin damar nazartar ayyukansu da suka gudana a shekarar domin samun damar bijiro da abinda ya kamata su yi a shekarar da aka shiga ta gaba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin babban Hafsan Tsaron kasar kasar nan Janar Gabriel Olanisakin, ya jaddada kudurin gwamnatin tarayya na kawo karshen aikin ‘yan kunar bakin wake a kasar nan.

A nasa bangaren gwamnan Jihar ta Oyo Abiola Ajimobi cewa ya yi Rundunar Sojin kasar nan ta cancanci yabo bisa kokarinta na tabbatar da tsaro da wanzuwar zaman lafiya a kasar nan baki-daya.

Daga cikin mahalarta taron bitar akwai babban Hafsan Sojojin kasar nan Laftanar Janar Tukur Buratai da Manjo Janar Ike Nwachukwu mai Ritaya da kuma Laftanar Janar Kenneth Minimah mai Ritaya

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!