Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya bukaci zaman lafiya a jihar Filato

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar jihar Filato da su zauna da juna lafiya.

 

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da shugabannin kabilu dana addinai jiya a gidan gwamnatin jihar ta Filato da ke garin Jos yayin wata ziyarar jaje da ya kai game da kashe-kashen da ke wakana a jihar a baya-bayan nan.

 

Ya ce jami’an tsaro ba za su gajiya ba har sai sun tabbatar da cewa dukkannin wadanda ke da hannu cikin kashe-kashen da ke wakana a jihar ta Filato dama kasa baki daya an gurfanar da su gaban kuliya.

 

Da yake gabatar da nasa jawabi gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo musu dauki don magance matsalar tsaro a jihar.

 

Rahotanni sun ce daya daga cikin shugabannin kabilun Birom da ke wajen taron ya bayyana cewa, suna zargin cewa maharan bakin haure ne ba ‘yan kasar nan bane.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!