Labarai
Shugaba Buhari ya umarci attorney Janar ya tsara dokar mayar da 12 ga watan Yuni ranar dimukuradiyya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci attorney Janar kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya tsara dokar da zata mayar da ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ta zama ranar dimokuradiyya ta kasa.
Tun a ranar Larabar da ta gabata ne dai shugaban kasar ya ayyana ranar 12 ga watan na Yuni ta zama ranar dimokuradiyya ya kuma baiwa wanda ake zargin cewa shi ya lashe zaben na June 12 a shekarar 1993 Moshood Abiola babbar lambar yabo ta GCFR.
Haka kuma shugaban kasar ya baiwa mataimakin Abiolan wato Ambassador Baba Gana Kingibe da kuma shahararren lauyan nan Gani Fawehini labar girma ta GCON
Ta cikin sanarwar da mataimakin shugaban kasa na musamman kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar ta ce ana sa ran ministan shari’ar zai yi gaggawar aikata abinda aka sa shi.
Bayyanar wanna labari ne dai ya karade kunnuwan al’umma a kasar nan tun a daren Larabar da ta gabata inda shugaban kasar ke ta samun yabo da suka daga al’umma daban-daban a fadin Najeriya.