Connect with us

Labarai

Shugaba Buhari ya yi sammacin gwamnan Katsina

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sammacin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, sakamakon ci gaba da kashe-kashen ‘yan bindiga da ke gudana a jihar.

Da ya ke tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a daren jiya Laraba bayan tattaunawa da shugaban kasa, gwamna Aminu Masari, ya ce, matsalar ‘yan bindiga a jihar, ya yi munin gaske, lamarin da ya sa manoma a yankunan da lamarin ya fi kamari ba sa ziyartar gonakin su.

A cewar gwamna Masari, yanzu sun gamsu cewa, ‘yan bindigar ba wai kawai barayin Shanu bane domin kuwa irin shirin da suke da shi wajen aikata ta’addan cin su, ya fi karfin a ce barayin shanu ne.

A baya-bayan nan ne dai, ‘yan bindga suka kashe mutane da dama a jihar ta Katsina, lamarin da ya sa, wasu al’ummar jihar suka gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar dauke da gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,817 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!