Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ministoci kan su je majalisun dokokin tarayya don kare kasafin kudi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci ministoci da shugabannin hukumomi da sassan gwamnati da su je gaban majalisun dokokin tarayya domin kare kunshin kasafin kudin su.

Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a karshen taron da ya yi a Alhamisdin da ta gabata a fadar Asorok da shugabannin majalisun dokokin tarayya karkashin jagorancin shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki.

Da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala taron, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce shugaba Buhari ya umurceshi da ya sanar da ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnati game da batun kunshin kasafin kudin.

Ya ce manufar shirya taron ita ce kara fahimtar juna tsakanin bangaren zartaswa da bangaren majalisa.

A cewar sa yayin taron shugaban kasar ya kuma yiwa shugabannin majalisun dokokin tarayyar, karin haske kan lamuran tsaro da tattalin arziki da kuma samar da aikin yi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,746 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!