Connect with us

Labaran Kano

Talauci ya sa wata mata cire da sayar da kayan wata yarinya

Published

on

Wata matashiya da har kawo yanzu ba a kai ga gano ko wacece ba ,a unguwar Gayawa a hukumar Ungogo, ta kama wata ‘yar karamar yarinya tare da tube mata tufafi.

 

,Al’amarin da ya sa ake zargin cewa ta cire mata kayan ne domin ta sayar sakamakon tsananin talauci da matashiyar ke fama da shi.

Da yake tabbatar wa Freedom Radio faruwar lamarin, mahaifin yarinyar Malam Auwalu Ya’u Akushi, ya ce  mahaifiyar yarinyar ta yi mata kwalliya ne da nufin zuwa gidan suna a bayan gidansu, sai dai tana fitowa ne sai matashiyar ta dauke ta.

Auwalu Ya’u Akushi, ya kara da cewa bayan matashiyar ta tube  kayan yarsa ne ta sako ta inda ta dawo gida ba tare da kayan da aka sanya mata ba.

Mahaifin yarinyar ya ce sun yi duk mai yiwuwa wajen gano matashiyar da ta tube kayan “Yar tasa  amma har kawo yanzu hakansu bata cimma ruwa ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,801 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!