Labarai
Bollywood: Uba da ‘dansa zasu fito cikin fim guda
Uba da da zasu futo tare a karon farko a tarihi wato jarumi Jakie Sharoff da Tiger Sharoff a cikin sabon film din Baaghi kashi na uku.
A yau Alhamis ne aka kammala Aikin sabon Film din BAAGHI kashi na uku wanda manyan jarumai zasu fito a cikin fim din irin su Shradda Kapoor da RITEISH DESHMUKH da sauran su.
Manyan jaruman dai Sun hadu a garin Jaipur inda suka yanka Cake Saboda nuna murna da farin cikin su da Kammala aikin fim din da suka yi.
Ana saran Mahaifin jarumi Tiger Shroff wato Jarumi JACKIE SHAROFF shima zai yi fitowa ta musamman wanda hakan ya nuna cewa haduwa ce a karo na farko ga Uba ga Da a cikin film tare.
Sabon fim din dai na Baaghi kashi na uku zai fita ne a ranar shida ga watan Maris din shekarar 2020 kamar yadda mai Shirya fim din Sajid Nadiadwala da Kuma mai bada umarnin film din Ahmed Khan suka shaida.
Rubutu daga,
Abdulkarim Muhammad Tukuntawa