Labarai
Tsaftace muhalli: Za mu gayyaci mahukuntan kasuwar Abbatuwa – Nasir Garo
Maikatar muhalli ta jihar Kano ta ce, za ta gayyaci mahukuntan kasuwar Abbatuwa don tattaunawa da su kan yin biyayya ga dokar tsaftar muhalli.
Kwamishinan muhalli Nasiru Sule Garo ne ya bayyana hakan ranar Asabar, jim kaɗan bayan kammala duban tsaftar muhalli na karshen wata ƙwaryar birnin Kano.
A cewar sa, lokacin da ya kamata mutane su zauna a gida, a lokacin ƴan kasuwar ta Abbatuwa suka fito cin kasuwa.
“Mun lura ƴan kasuwar duk sun fito sun yi cirko-cirko suna jiran lokaci ya yi su fara cin kasuwa, wanda kuma yin haka ya saɓa dokar tsaftar muhalli” a cewar Garo.
Kwamishinan ya kuma , “Don haka na bada umarnin aje a zauna da shugabannin ƙungiyar kasuwar ta Abbatuwa don tattaunawa da su ga me da dokar mu, domin kuwa idan muka sake samun su da wannan laifi hukunci zai hau kansu”.
Haka kuma yayin duban tsaftar muhalli Nasir Sule Garo ya nuna takaicinsa kan yadda mutane suka riƙa fitowa maimakon zama a gida kamar yadda aka tsara.
Har ma ya nuna damuwa kan halayyar da wasu matasa suke nunawa a kowanne ƙarshen wata na yin ƙwallon ƙafa a kan tituna, yana mai cewa ba za su lamunci hakan ba.
Tuni dai kotun tafi da gidanka mai kula da tsaftar muhalli ƙarƙashin mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ta yanke hukuncin tara nan take ga waɗanda suka karya doka
You must be logged in to post a comment Login