Connect with us

Labarai

Tsohuwar matar Nelson Mandela ta rasu

Published

on

Tsohuwar mai dakin marigayi Nelson Mandela, wato Winnie Mandela ta rasu yau.

Winnie Mandela wadda ta auri marigayi Nelson Mandela lokacin da yake zaune a gidan kaso na tsibirin Robben ta rasu tana da shekaru tamanin da daya.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakiyar ta, ta musamman Zodwa Zwane ta fitar yau litinin.

Sanarwar na zuwa ne kusan watanni uku kenan da aka samu labarin kai marigayiyar wani asibiti da ke Johannesburg, sakamakon matsalar ciwon koda da take fama da ita, inda daga nisani kuma iyalan ta suka sanar da samun lafiyar ta.

Har yanzu dai sanarwar bata bayyana dalilin mutuwar Winnie Nelson Mandela ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,762 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!