Labarai
Wajibi iyaye su tashi tsaye wajen tarbiyar ‘ya’yan su -Sarkin Alkalma
Sarkin Alkalman Kano Alhaji Iliyasu Labaran Daneji yace matukar Iyaye suna so a magance matsalar tabarbarewar tarbiyyar ‘ya’ya a wannan zamani ya zama wajibi iyaye su tashi tsaye wajen ganin yaran su sun sami ingantaccen Ilimin Addinin musulunci.
Alhaji Ilyasu Daneji ya bayyana hakan ne lokacin saukar Karatun Al’qur’ani mai girma karo na biyu na Makarantar Shabbabu Rasulillah Islamiyya dake Unguwar Nalado dake Tukuntawa a yankin Burnin Kano.
Sarkin Alkalman Kano Alhaji Ilyasu Daneji ya kara da cewa abun takaici ne yadda tarbiyya a yanzu tayi karanci a tsakanin matasa wanda hakan ke da nasaba da rashin tsayawar iyaye kai-da-fata-wajen sanya ‘ya’yan su a makaranta domin neman Ilimi.
Da yake jawabi shugaban Makarantar Malam Musbahu Saleh kira yayi ga masu hannu da shuni dasu kawowa makarantar dauki kasancewar makarantar ta shafe sama da shekaru 27 a duniya amma har yanzu bata dena fuskantar matsalar rashin abun zama da muhalli ba.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa malamai da dama ne suka halarci taron bikin saukar da sauran al’ummar gari na dalibai bakwai maza da mata wanda suka sami damar sauke karatun Al’kur’ani mai girma a makarantar a yau.