Connect with us

Manyan Labarai

Wasu al’ummar Makarfi sun cike ramukan titun Kaduna zuwa Kano na tsawon kilomita dari

Published

on

 

Wasu al’ummar karamar hukumar Makarfi dake Jahar Kaduna sun cike ramukan titin Kaduna zuwa Kano da yakai tsawon kilomita 100 daga yankin Zariya zuwa garin Tarau na jihar Kano.

Da yake tattaunawa da Freedom Radio wanda ya jagoranci cike ramukan da ke sanadin asarar rayukan al’umma ,Dauda Musa yace sun dauki gabarar aikin ne  inda suka cike ramukan da ya taba sanadin mutuwar mutane goma sha takwas.

Yace a halin yanzu sun kashe Naira dubu dari biyar domin yin aikin.

Dauda Musa yace lalacewar ramukan ya matukar tayar musu da hankali wanda hakan yake sanadin asarar rayukan al’ummar da ke bin hanyar

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!