Labarai
Wasu gwamnatoci na yin burus da umarnin kotu- Barista Ibrahim Sule
Barista Ibrahim Sule ya ce rashin bin umarnin kotu da wasu gwamnatoci da masu madafan iko a kasar nan ke yi na taka rawa wajen ta’azzara ala’amurran shari’a a kasar nan.
Ana dai zargin masu rike da madafun iko da take umarnin kotu wajen yin yadda suka ga dama ko da kuwa kotu ta yanke hukunci kan wani al’amari da ya taso.
Barista Ibrahim Sule daga makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya shiyar Kano dake Bagauda ne ya bayyana hakan a cikin shirin duniyar mu a yau na nan gidan Redoyi Freedom wanda ya mayar da hankali kan yadda ake yi kememe da bin umarnin kotu.
Baristan ya kuma kara da cewar kuto na da hurimin da zata zartar da hukunci a kan kowa ne al’amari da ya taso tsakanin al’umma kuma ya zama wajibi abi umarnin ta.
Kotun daukaka kara ta sanya ranar shari’ar Ganduje da Abba
Kotu ta yankewa matashi hukuncin kisa a Kano
Dole masu ruwa da tsaki su amince da hukuncin kotuna -Sarkin Kano
A nasa bangaran Kwamared Bala Abdullahi, daga Kungiyar nan dake rahin kare hakin dan adam ta Network For Justice ya bayyana cewar abinda ya sanya kasar nan ke fuskantar wannan matsalar baya rasa nasaba rashin nagartatun shugabanni.
Bakin sun karkare shirin da cewar muddin ana son kawo karshen wannan matasala ya zama wajibi al’umma su rika sanin irin mutanen da zasu zaba.