Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Wata gobara ta kone dakuna 25 da shaguna 12 a birnin Illorin, jihar Kwara

Published

on

Wata gobara da ta tashi a Unguwar Ola-Oti da ke garin Kankatu a birnin Ilorin Jihar Kwara, ta yi sanadiyyar kone dakuna 25 da kuma shaguna 12 a jiya Litinin.

Wani ganau ya shaidawa manea labarai cewa gobarar ta fara ne da karfe biyu na tsakar daren Lahadi sannan ta shafe tsawon sa’o’i 4 tana ci kafin jami’an kashe gobara na Jihar su kawo karshenta.

Duk da cewa babu wani mutum guda da gobarar ta illata a yankin, sai dai ta yi sandiyyar kone kadarori na miliyoyin nairori tare da raba mutane da dama da gidajensu.

Har yanzu dai babu tartibin bayanin makasudin faruwar gobarar, sai dai babban jami’in kare aukuwar gobara a a Jihar ta Kwara Alhaji Abdulwahid Yakubu ya ce mai yiwuwa wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!