Labarai
Yajin aiki: Ɗaruruwan fasinjoji na yin tattaki da ƙafa
Ɗaruruwan fasinjoji a Kano na ci gaba da yin tattaki tun daga safiyar yau Litinin, sakamakon yajin aikin direbobin babur mai ƙafa uku.
Fasinjojin dai sun yi cirko-cirko a bakin titinan Kano domin neman abin hawa da zai kai su zuwa wuraren gudanar da ayyukan su na yau da kullum.
Sai dai rashin babur mai ƙafa uku ya tilastawa mafi yawa daga cikin fashinjojin yanke shawarar yin tafiya da ƙafa domin isa inda suka nufa.
Ga dukkan alamu dai hakan na nuna yadda aka dogara da babura masu ƙafa uku wajen yin sufuri a Kano
Cikin fasinjojin da rashin babur mai ƙafa ukun ya shafa har da ɗalibai da ƴan kasuwa da ma’aikata, musamman yadda aka wayi gari a yau da komawa makaranta bayan hutun zangon karatu na farko da ɗlaibai suka tafi.
Hakan ya haifar da rashin zuwan mafi yawa daga ɗalibai da malamai makarantu, yayin da yajin aikin ya shafi jarrabawar wasu ɗalibai a manyan makarantun ƙasar nan, baya ga hana ma’aikata zuwa guraren aikin su.
You must be logged in to post a comment Login