Labarai
Yajin aikin ƴan adaidaita sahu: hukuncin KAROTA ya saɓa doka – Barista Abba Hikima
Wani lauya me zaman kansa anan Kano ya ce, hukuncin da hukumar KAROTA ta yi ga matuƙa baburan a daidaita sahu na biyan kudin haraji duk shekara ya saɓa da tsarin doka.
Barista Abba Hikima Fagge ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Nasir Salisu Zango ranar Litinin.
Lauyan ya ce, duk da dokoki sun bai wa hukumar KAROTA dama ta karɓi haraji ko kuma ta bada lasisin tuƙi amma babu inda doka ta ce duk shekara sai sun biya kuɗi.
“Wannan abu bai dace ba, duba da yadda ake fama da matsin tattalin arziƙi Wanda yin hakan na iya kawo musu naƙasu a cikin harkar kasuwancin su”.
Baresta Abba Hikima Fagge ya kuma ce, dokar na magana ne akan idan matuka baburan sun biya sau ɗaya ya wadatar, la’akari da yadda baburin baya daɗewa kuma ba wani abu suke samu sosai ba.
You must be logged in to post a comment Login