Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yansanda sun kama wani matashi mai garkuwa da mutane

Published

on

Yan sanda a jihar Gombe sun kama wani matashi dan shekara 19 mai suna Mohammad Ahmad da ake zargi da garkuwa da mutane mazaunin unguwar Gabukka a jihar Gombe.

Matashin dai wanda ake zargin ya sace wani dan shekara bakwai Hassan Abubakar dake unguwar Kumbiya-kumbiya, a jihar ta Gombe.

An kama mai garkuwa ne bayan da yayi basaja ya fito a matsayin dan kasa na gari tare da dawo da yaron da aka sace na tsawon kwanaki uku.

Sai dai rikici ya barke ne dai bayan da mahaifin yaron da aka yi garkuwa da shi yaki amincewa da biyan kudaden fansan dan na sa da aka bukata na naira miliyan 3.

Yayin da ake holen masu garkuwan a gaban manema labarai a jiya Alhamis, kakakin rundunar yan sanda ta jihar SP Mary Malum ta bayyanawa jaridar Punch yadda abin ya faru.

Ta ce Ahmad ya tafi unguwar kumbiya-kumbiya inda ya tarar da yaron yana alwala a masalaci ya kuma aike shi da ya sayo masa pure water, daga bisani kuma ya bi shi a baya ya kuma dauke shi a kan babur inda ya kai shi gidansa.

Bayan ya shafe kwananki ukun ne kuma ya lura da iyayen yaron basu da niyya biya ne, ya yanke shawarar kiran kawun yaron Aminu Babayo tare da cewa ya tsinci yaron a unguwar Gabbuka.

RUBUTUKA MASU ALAKA:

Yan bindiga dadi sunyi garkuwa da mutane 8 a jihar Kaduna

Dino Melaye ya gabatar da kudiri kan masu garkuwa da mutane

Lokoja-Rundunar tsaron civil defence tayi holin wasu masu satar mutane domin garkuwa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!