Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

YUMSUK ta ƙara wa’adin rubuta jarrabawar ɗalibai a gobe

Published

on

Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke nan Kano ta dakatar da dukkan jarrabawar da ɗalibai za su rubuta a yau, da kuma wadda za a rubuta da ƙarfe 8 na safiyar gobe talata.

To sai dai ta ce a jarrabawar gobe talata ta ƙarfe 11:30 na safe zuwa ƙarfe 2:30 da kuma ta ƙarfe 3 na rana zuwa ƙarfe na yamma tana nan daram kamar yadda aka tsara.

Wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na jami’ar Abdullahi Abba Hassan ya fitar yau, ta ce jami’ar ta amince da samar da motocin bas-bas domin ɗaukar ɗalibai daga wasu wuraren domin kai su makaranta tare da mayar da su.

Sanarwar ta ƙara da cewa nan gaba kaɗan za ta sanar da lokacin rubuta jarrabawar da aka ɗage.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!