Labarai
Za mu ƙirƙiro hanyoyin da zasu inganta harkar Noma da kiwo-MD KNARDA
Gwamnatin jihar Kano ta ce lokacin da ta karɓi gwamnati ta sami hukumar bunƙasa noma da raya karkara ta Knarda a cikin mawuyacin halin, kasan cewar yadda ma’aikatan hukumar basa son zuwa aiki,
Sai dai kawo wannan lokacin hukumar ta fito da hanyoyin gyara domin farfaɗo da hukumar, inda yanzu haka aka cimma nasara wajen daukar saitin ma’aikata.
Shugaban hukumar Dakta Farouk Kurawa ne yayi wannan jawabin yayin da yake ganawa da manema labarai kan irin kalubalen da hukumar take ciki kafin karɓar sa da kuma irin nasarar da suka samu zuwa yanzu.
Haka zalika Dakta Farouk Kurawa ya ce wannan hukumar tana kula da yadda za’a gudanar noma da bayar da horo ga malan gona, yadda ya kamata domin samin anfanin gona a faɗin jihar kano dama ƙasa baki ɗaya.
Kurawa ya ce yanzu haka suna tuntubar hukumomi daban daban na gwamnatin tarayya domin bayar da tallafi ga jihar kano wanda zai anfani jihar da manoma baki ɗaya.
Haka kuma yanzu haka muna haɗa ƙididdigar manoman da suke jihar Kano domin tabbatar da kasafi akan harkar noma.
Mun ɓuƙaci gwamnatin tarayya ta ware kudi kaso 70 cikin ɗari wajen inganta harkokin malaman gona wanda haka zai inganta harkar noma a faɗin ƙasar nan A cewar Kurawa.
Akwai hukumomi da suke gudanar da ayyuka, mun shiga aiki da su domin koyar da mata sana’o’in daban daban na noma da sarrafa anfanin gona wanda ya shafi gyada,masara da dai sauran kayan anfanin gona.
Akwai tsarin bayar da kayan kiyo ga mata a faɗin jihar Kano wanda yanzu haka wannan tsari yayi nisa a faɗin jihar domin samar da kayan kiwo a faɗin jihar Kano. haka zalika wannan shirin zai samar da mayanka a dukkanin kananan hukumomi na Kano domin tsaftace harkar yanka dabbobi.
Yanzu haka akwai shirin tallafawa manoma da taki iri daban-daban domin samar da anfanin gona mai kyau a faɗin jihar Kano.
Kurawa yace yanzu haka akwai tsarin gyara hanyoyi a kasuwar hatsi ta Dawanau domin samin saukin zirga-zirga ababan hawa musamman masu dauko kayan hatsi.
Haka kuma zamu ci gaba da shigo da tsare-tsare wanda zai ƙara haɓakar harkar noma da kiwo a faɗin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login