Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Barka Da Hantsi

Za mu fara ɗaukar sabbin malamai – Gwamna Badaru

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce, za ta fara ɗaukan sabbin malamai a dukkanin ƙananan hukumomin jihar.

Kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar Alhaji Kabiru Hassan Sugungun ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na Freedom Radio.

Sugungun ya ce “Bayan shekara 30 da ƙirƙirar jihar, an samu nasarori a ɓangaren Ilimi da noma da kuma bunƙasa ƙananan hukumomi”

Alhaji Kabiru Sugungun ya ce, yanzu haka gwamnatin jihar na shirin ɗaukar malaman makaranta na wucin gadi a kowacce ƙaramar hukuma, waɗanda daga bisani za’a tabbatar da su a matsayin cikakkun ma’aikata.

“Baya ga wannan ma, mun bijiro da tsarin bai wa matasa aikin yi ta hanyar tantance su a cikin ƙananan hukumominsu na asali don rage zaman banza” a cewar Sugungun.

Haka zalika ya ce gwamnatin jihar tana tallafawa manoma don bunkasa tattalin arziki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!