Connect with us

ilimi

Za mu fara koyar da aikin kula da lafiya a jami’ar Yusuf Maitama Sule – Farfesa Kurawa

Published

on

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ce za ta bude tsangayar koyar da aikin lafiya a Jami’ar a shekara mai kamawa ta 2022.

Shugaban Jami’ar Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ne ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da sababbin daliban makarantar su dubu biyar da sittin, da ta dauka a zangon karatu na shekarar 2021/2022.

Ya ce Jami’ar za ta ci gaba da baiwa dalibanta ilimin da ya dace wanda daliban za su yi amfani da shi da zai taimaki kasar nan.

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya bukaci daliban da su zama jakadu na gari a ciki da wajen makarantar yayin da suke gudanar da karatun su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!