Labarai
Za mu samarwa da matasa hanyoyin dogaro da kai-Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ci gaba da mayar da hankali wajen koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai ba wai sai mutum ya jira aikin gwamnati.
Inda yanzu haka tsarin da Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yiwa cibiyar koyar da sana’o’i ta Dangote dake Dawakin Kudu zai ɗaga darajar Kano zuwa gaba.
Shugaban cibiyar Alkasim Husaini Wudil ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a wani ɓangare na ƙara horar da matasa sana’o’in dogaro da kai.
Alkasim Husaini Wudil ya kuma ce a baya wannan cibiyar a kulle take ba’a iya gudanar da komai a cikin ta illa kawai biyan mutane albashi ba tare da sunayin aiki ba.
Adan haka gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagoranci Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin gyara duk wata matsala domin farfaɗo da cibiyar dan samarwa da matasa hanyoyin da zasu dogara da kan su- a cewar Alkasim Husaini Wudil.
Haka kuma yanzu haka cibiyar ta fara aiki gadan gadan ga al’umma inda yanzu haka gwamnati ta samar mata da motocin da zasu dunga jigilar malamai da ɗalibai kyauta ba tare da biyan kuɗi ba.
Haka kuma cibiyar zata dunga yaye ɗalibai mataki mataki kan fannin kwarewar mutum.
Kuma yanzu haka wannan cibiyar ta tanadi duk wasu kayan aiki da za su koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai.
You must be logged in to post a comment Login