Labarai
Za mu tabbatar mun gyara dukkannin cibiyoyin koyar da sana’ar hannu dake fadin kano
Gwamnatin jihar Kano ta yi alƙawarin kammala aikin gyara dukkannin Makarantun fasaha dana horar da sana’o’in dogaro da kai da aka samar da su a shekarar 2011 a ƙananan hukumomi 44 nake faɗin jihar
Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yau yayin bikin ranar baje kolin fasahar matasa ta duniya da cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote dake ƙaramar hukumar Dawakin kudu haɗin gwiwa hukumar kula ilimin ƙananan yara ta duniya UNESCO.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce reƙe sana’o’in hannu wani jigo ne da zai bunƙasa aiyukan masana da samarwa da matasa aiyukan yi.
A nasa jawabin karamin ministan ma’aikatar cigaban matasa Mr. Ayodele Olawode ya yaba da harkokin cibiyar, inda ya ce ma’aikatar sa ta fito da shirin ilimartar da matasa miliyan 7 akalla sana’o’in dogaro da kai.
Da yake jawabin Shugaban Hukumar UNESCO ta ƙasar nan Abulrahman Diyalo ya ce za su yi haɗin gwiwa da gwamnatin jahar kano da cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote domin koyar da dubban matasa sana’o’in dogaro da kai.
Haka kuma gwamnan ya yi alƙawarin samarwa da cibiyar gidajen kwanan dalibai da biya musu kudin karatu da daukar nauyin kai su makaranta a kullum da kuma kulawa da walwalarsu.
You must be logged in to post a comment Login