Labarai
Za mu tabbatar mun kare Kano daga barazanar ambaliya – Gwamna Abba
Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da bayar da tallafin kayan aikin gayya ga kungiyoyi 160 dake faɗin kwaryar birnin kano domin tsaftace magudanan ruwa da suke lungu da saƙo na ƙananan hukumomi 8 dake cikin birnin, domin kaucewa daga barazanar ambaliya da masana ke hasashen cewa za’ayi a wannan shekarar.
Da yake ƙaddamar da bayar da kayan aikin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce samar da wannan kayan aikin zai taimaka wa unguwanni wajen fito da shara daga cikin magudanan ruwa domin tsaftace yankuna.
Gwamna Yusuf yayi kira ga kungiyoyin sa kai da zasu gudanar da wannan aikin da su tabbatar cewa wannan kayan da gwamnati ta basu ta basu ne a Matsayin wani tallafi da zasu bayar ga al’ummar jihar kano.
Haka kuma yace sauran ƙananan hukumomi dake wajen kano suma gwamnati ta bawa shugabanni riƙo na yankunan da su fara gudanar da wannan aikin a yankunan domin kaucewa barazanar ambaliya.
Daga ƙarshe gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa zai ci gaba da fito da tsare-tsaren da zasu samarwa da jihar Kano ci gaba a dukkanin ɓangarori daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login