Labarai
Zan ƙara wa ɗaliban Kano alawus – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bada umarnin a karawa daliban jihar Kano alawus da ta ke biyan su, kasancewar wanda a ke basu a yanzu ya yi musu kadan.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a ranar Asabar lokacin da ya halarci taron da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha ta shirya a wani bangare na bikin ranar matasa da majalisar Dinkin duniya ta shirya.
Gwamna Ganduje ya ce, Kudurin da majalisar Dinkin duniya ta yi na cewa a rinka sanya matasa a al’amuran ci gaba na duniya tuni jihar Kano ta yi nisa a wannan bangaren.
Haka zakila, da yake jawabi a yayin da ya ziyarci duba aikin gyare-gyare da a ke yi a hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa, Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gadon da ya ci gaba da gudanar da aikin yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata ba tare da dagawa dukkan wanda a ka samu da cin hanci da rashawa kafa ba.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa, Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma ce, a na gyare-gyare a hukumar ne domin sama musu kyakkyawar muhalli da zai sa su rinka gudanar da ayyukan su cikin nutsuwa.
You must be logged in to post a comment Login