Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƙawata birane: An fara dakatar da kwantena da shaguna da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Published

on

Hukumar ƙawata birane ta jihar Kano ta fara aikin dakatar da shaguna da kwantena da aka dasa su ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar ta ce, an fara aikin ne bisa umarnin gwamna Dakta Abdallahi Umar Ganduje.

Dakatar da kwantena da shagunan da aka yi su akan hanya ba bisa ƙa’ida ba wani yunƙuri ne na tsaftace Kano da kuma tsara ta yadda ya kamata.

Hakan na cikin sanarwar da mai baiwa shugaban hukumar shawara kan harkokin ƙawata birane Kwamared Abdulkarim Kowa Naka ya fitar.

A cewar sa, hukumar za ta bi duk guraren da aka samar da su ba bisa ƙa’ida ba don ganin an ɗauki mataki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!