Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƙorafi: Mun wayi gari mun ga ana aune mana gidaje da filaye – Al’ummar Madob

Published

on

Al’ummar kauyukan Gidan Guda, Rugar Kuyan, Galadimawa da Kafin Agur, sun koka kan yadda suka ce sun wayi gari da ganin wasu ma’aikata suna aune musu gidaje da gonaki.

Al’ummar dai sun bayyana cewa akwai barazana mai yawa ga rayuwarsu kasancewar basu san wanda yake da alhakin aune musu gonaki da gidajen ba.

Wasu daga cikin mazauna wadannan yankuna da aikin ya shafa sun ce “Kawai mun wayi gari mun ga wasu mutane da bamu san ko su waye ba suna ta auna gidaje da filayen tare da sayar da su ga wasu da bamu sani ba”.

“Kuma babu wanda ya nemi izinin mu ko tuntubar mu kasancewar dukka gidaje da filayen muallakin mu ne” a cewarsu

A kan wannan zargi da al’ummar suka yi ne wakilinmu Yakubu Musa Kanwa ya ya tuntubi shugaban karamar hukumar ta Madobi Muhammad Lawan Yahaya wanda ya ce shi ba zai ce komai a kan batun ba, illa kawai zai hada mu da jami’an hukumar kula da filaye.

Kawo yanzu dai da muke hada wannan rahoton bai neme mu ba, sai dai za mu ci gaba da bibiyayar wannan lamari domin gano wanda yake da alhaki kan lamarin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!