Labarai
Ƙungiyoyin matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/12/58a27a43-34bf-4503-b95a-9cc909fbd75b.jpg)
Ƙungiyoyin matasa sun gabatar da zanga-zangar lumana domin nuna damuwarsu bisa yawaitar kashe kashen mutane a Arewacin ƙasar nan.
Matasan ɗauke da kwalaye kunshi da rubutu da ke nuna buƙatar a kawo karshen kashe-kashen mutane a Arewa sun yi dandazo ne a bakin harabar sakatariyar ƙungiyar yan jaridu anan Kano.
Guda daga cikin jagororin zanga-zangar Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana cewa sun fito cikin zanga-zangar lumana ne kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya baiwa kowannne ɗan Najeriya dama.
Zanga-zangar dai ta biyo bayan yadda ake ƙara samun kashe-kashen al’ummar da basi-ji ba-basu-gani ba a wasu jihohin ƙasar nan musamman ma na yankin Arewa.
You must be logged in to post a comment Login