Labarai
Ƴan baro dake kasuwar sabon Gari sun gudanar da zanga-zanga
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2024/03/IMG-20240327-WA0017_1.jpg)
Ƙungiyar ƴan baro dake kasuwar sabon gari anan kano sun gudanar da zanga-zangar lumana akan titin gidan Gwamnatin jihar, inda suke zargin shugabancin kasuwar da tilasta musu tashi daga guraren da suke gudanar da kasuwancin su a kasuwar, inda suka ce hakan na barazana da rayuwar su.
Shugaban ƙungiyar Tasi’u Ibrahim ne ya jagoranci zanga-zangar lumana a yau inda suke kira ga mahukunta wajen duba halin da zasu shiga idan har aka tilasta musu tashi a wannan lokaci.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan zanga-zangar, Shugaban kasuwar ta sabon Gari Alhaji Abdul Bashir Hussain yace ba wai haka kawai aka ce su tashi ba sai da shugabancin kasuwa ya zauna, domin samar kyakkyawan tsari a cikin kasuwar.
Haka kuma la’akari da yadda kasuwar ta cunkushe ya sanya dole ayi tsarin da zai samar da rage cucewar kasuwar shiyasa aka dau wannan mataki, a cewar shugaban kasuwar.
Haka zalika shuagabancin kasuwar yace akwai tsarin da akayi musu wajen daina shigowa da baro cikin kasuwar domin rage cinkoson da yake a kasuwar.
You must be logged in to post a comment Login