Connect with us

Labarai

Ƴan bijilanti sun fafata da masu garkuwa da mutane a Kano

Published

on

Jami’an sintiri na Bijilante a nan Kano sun ƙwato wasu mutane huɗu daga hannun masu garkuwa da mutane a ƙauyen Gammo da ke ƙaramar hukumar Sumaila.

Shugaban ƴan Bijilante na jihar Kano Muhammad Kabir Alhaji ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Shugaban ya ce, sai da suka yi ɗauki ba daɗi tsakanin masu garkuwar kafin daga bisani suka yi nasara.

Wasu bata gari sun kai wa ‘yan sintiri na Vigilante hari a Kano

Kungiyar ‘yan Sintiri ta Vigilante ta bukaci gwamnatin Kano ta samar da hadin kai tsakanin Kamfanoni masu zaman kansu don samar da Asusun tallafawa jami’an tsaro

Alhaji Kabiru ya ce cikin mutanen da aka sace din hudu mata ne, kuma sun yi nasarar kwato guda biyu daga cikin su.

Kabiru Alhaji ya ce, tuni suka miƙa wanda suka kuɓutar zuwa ga rundunar ƴan sandan jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!