Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun sace hakimi a Neja – Ƴan sanda

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta tabbatar da sace hakimin Wawa Dakta Mahmud Aliyu, a karamar hukumar Borgu ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawar sa da manema labarai.

Ya ce, ƴan bindiga sun yi garkuwa da hakimin daga fadarsa a daren Asabar da misalin karfe 10.

Abiodun ya ce tuni ƴan sanda sun fara bin sawun ƴan bindigar don ceto hakimin da kuma gano maɓoyar su.

Har ma ya buƙaci mazauna yankin da su tallafawa hukumomin tsaro da bayanan sirri don yaƙi da masu garkuwa da mutane a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!